fidelitybank

Gina Kasa: ‘Yan Najeriya ku ci gaba da marawa Buhari baya – Orji Kalu

Date:

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a kokarinsa na sake dawo da kasar nan.

Da ya ke karin haske game da nasarorin da shugaban kasar ya samu, tsohon gwamnan ya jaddada cewa shugaba Buhari ya himmatu wajen ganin ko da ci gaban kasar ne, ya kara da cewa farfado da ababen more rayuwa a yankin Kudu maso Gabas ba zai yi wu ba idan shugaban ya nuna son kai ga Ndigbo.

Kalu a yayin da ya ke gargadin ‘yan siyasa da su guji kalaman kyama da kamfen na zage-zage ga shugaban kasa, ya nuna cewa shugaba Buhari ya cancanci yabo daga ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini da siyasa ba.

Tsohon Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a lokacin da ya karbi tawagar masu ruwa da tsaki na Isi Ugwu a ziyarar hadin kai a Abuja, kamar yadda mai taimaka masa a yankin Arewa, Aminu Shehu Uba Sharada ya aikewa manema labarai.

Ya ce, “Na yi farin ciki da ziyarar masu ruwa da tsaki daga Isi- Ugwu da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia. Kamar yadda ku ka ambata, ayyukan tituna da sauran ababen more rayuwa da a ke aiwatarwa a gundumar Abia ta Arewa ba za su iya yi wu ba sai da goyon bayan shugaba Buhari. Ina da kwarin gwiwa na saukaka ayyuka zuwa gundumar Abia ta Arewa, saboda goyon bayan da shugaban kasa ya ba ni”. Inji Kalu.

“Gwamnatin tarayya ta APC karkashin jagorancin shugaba Buhari ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gina ababen more rayuwa a shiyyoyi shida na kasar nan. Shugaban kasa ya cancanci a yi mana addu’a kamar yadda Allah ya kaddara masa ya jagoranci ‘yan Nijeriya da Nijeriya.

 “Littattafai masu tsarki sun jaddada cewa ya kamata mu yi wa shugabanninmu addu’a, domin haka dole ne mu kiyaye ka’idojin Littafi Mai Tsarki da Alkur’ani mai tsarki. A ko da yaushe na ci gaba da tabbatar da cewa shugaba Buhari ya na goyon bayan kungiyar Ndigbo da ma Najeriya baki daya. Idan a ka yi la’akari da ayyukan da gwamnatin tarayya ta tabbata a yankin Kudu maso Gabas da sauran sassan Najeriya, a bayyane ya ke cewa shugaban kasa ya himmatu wajen gina kasa mai albarka. Shugaban kasa dan Najeriya ne mai tsananin tawaya kuma mai kishin kasa”. Inji Kalu.

Tsohon Gwamnan ya kuma yabawa tawagar bisa wannan ziyarar, inda ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen samar da rayuwa mai ma’ana ga al’ummar mazabar sa.

sahara hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp