fidelitybank

Gidauniya ta za ta mayar da kai wajen koyar da wasanni da samar da ilimi a Najeriya – Dan wasan Dortumnd

Date:

Ɗanwasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Dortmund da ke Jamus, Karim Adeyemi ya buɗe gidauniya a Najeriya.

Adeyemi, wanda yanzu yake wakiltar tawagar ƙasar Jamus, asalinsa ɗan Najeriya, kasancewar mahaifinsa ɗan Najeriya ne.

Ya buɗe gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke jihar Oyo, ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi.

A kwanakin baya da ya ziyarci Najeriya, Adeyemi ya shaida wa BBC cewa nan gaba yana tunanin komawa taka leda a gasar Premier ta Ingila.

A gasar zakarun turai ta bana, ɗanwasan ya zura ƙwallo uku rigis a ragar ƙungiyar Celtic a wasan da suka fafata.

A game da gidauniyar, ya ce, “na san yadda rayuwa take a nan Najeriya da kuma yadda rayuwa take a Jamus. Na daɗe ina da tunanin idan na samu ɗaukaka ta hanyar ƙwallon ƙafa, zan koma asalina a Najeriya in taimaka wa mutane. Ba zan taɓa mantawa da asalina ba. Wannan babban abin alfahari ne,” in ji shi.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu Tinubu bai nada Jakadun Najeriya ba – ADC

Jam’iyyar ADC ta soki yadda gwamnatin APC ta shugaba...

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...
X whatsapp