fidelitybank

Gidan Yarin Liberia ya daina karbar masu laifi saboda cinkoso

Date:

Babban gida yarin Monrovia da ke Liberia ya fara daina karɓar ɗaurarun da ake turo masa saboda cikar da ya yi da kuma fargabar ɓarkewar cututtuka.

Minsitan harkokin Shari’a na Liberia Frank Musa Dean ne Ya shaida wa BBC cewar waɗanda aka ƙi karɓar su ana zargin su ne da aikata ƙananan laifuka.

“Idan ba a yi wa wani rauni ko illa ga wani ba, mutanen da aka tsare kan ƙananan laifuka, yanzu za su koma gida sai masu unguwanninsu su dinga sa ido a kansu.

Hakan dai ya biyo bayan rahotanin da wasu daga cikin kafafen yaɗa labaran kasar suka yi na yadda masu gadin gidan yarin ke ƙin amincewa da karɓar sababbin ɗaurarun, saboda yajin aikin da suke yi kan jikirin biyansu albashi.

Sai dai shugabannin gidan yarin sun musanta hakan.

An gina gidan yarin ne da zummar ɗaukar mutum 300, a lokacin da adadin mutanen Monorovia bai wuce dubu 300 ba.

Sai dai a yanzu yana dauke da mutum 1,600, yayin da adadin mutanen Monorovia ya kai miliyan daya da rabi.

Wandan ke zaune a gidan yarin sun hada da waɗanda aka yanke wa hukucin kisa da masu fashi da makami.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp