Gidan tarihin Birtaniya y mayar wa da masarautar Benin tagulla biyu, fiye da karni ɗaya da sojojin Birtaniya suka yi awon gaba da su, matakin da ake ganin zai buɗe ƙofar dawo da dubban kayayyakin tarihi zuwa asalinsu a Najeriya.
Kayayyakin da sojojin Birtaniya suka sace a 1897, yawancinsu suna gidajen tarihin ƙasashen Yammaci da kuma wasu gidajen tarihin masu zaman kansu.
Masu bincike da ƴan mulkin mallaka ne yawanci suka sace kayayyakin tarihin. In ji BBC.
Tagullan Benin da dubban kayan ƙere-ƙere na al’adu da mutum-mutumi da hauren giwa, sun kasance alamu da ake zargi na rashin adalci. Asalinsu daga yankin da ake kira jihar Edo ne a yanzu a Kudancin Najeriya.
An yi ƙasaitaccen biki na tarɓar tagullan guda biyu da aka dawo da su a masarautar Benin.
Akwai wasu da dama da ake tunanin an adana su a New Zealand da Amurka da kuma Japan.
Tun a watan Oktoba Jami’ar Aberdeen ta miƙa tagullan guda biyu ga ofishin jekadancin Najeriya.
A na tunanin akwai kashi 90 na kayayyakin tarihi na Afirka da ke gidan tarihin Turai a Faransa da kuma gidan tarihin Birtaniya na London.
Gidan tarihin Birtaniya, da ke da kayan tarihin Benin 950, ya sha suka musamman saboda ƙin amincewa ya dawo da su, amma yana ɗaya daga cikin gidajen tarihin da ke ƙoƙarin tabbatar kayayyakinsa a bisa doka.