Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya, COREN, ta ce an samu rugujewar gine-gine 22 tsakanin Janairu zuwa Yuli 2024 a ƙasar nan.
Shugaban COREN, Farfesa Sadiq Abubakar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Taron manema labarai mai taken, “Rugujewar Gine-gine a Najeriya a Kwanakin baya: Kira don Dorewar Haɗin Kai daga Duk Masu ruwa da tsaki.”
A cewar Abubakar, daga watan Janairu zuwa 14 ga watan Yuli kadai, an samu rahoton rushewar gini har sau 22 a Najeriya, inda Legas ke da kashi 27.27, Abuja da Anambra na da kashi 18.18 cikin 100 kowanne.
Ya kuma bayyana cewa Ekiti da Plateau sun biyo baya da kashi 9.09 kowanne, sannan jihohin Kano, Taraba, da Neja na da kashi 4.55 kowanne.
“Haka zalika, bayanai sun nuna cewa Legas ce ke kan gaba wajen rugujewar gine-gine.
“A gaskiya, sama da gine-gine 91 ne suka ruguje, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 354 a Legas daga shekarar 2012 zuwa yau.
“Hakazalika, a Abuja, kimanin gine-gine 30 ne suka ruguje daga shekarar 1993 zuwa yau, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 64 tare da jikkata wasu da dama.
“Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan na rushewar gini a kusa da DMGS Onitsha, Jihar Anambra, a ranar 12 ga watan Yuni da na wata makaranta (Saint Academy) da ke Filato a ranar 13 ga Yuli, inda dalibai 22 suka mutu, 134 suka jikkata, da kuma rushewar ginin a ranar 13 ga watan Yuli. Kubwa, Abuja,” ya kara da cewa.
Shugaban na COREN ya ce abubuwan da suka faru suna da ban tsoro, yana mai jaddada cewa suna kira da a zurfafa tunani da hadin gwiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki wajen dakile bala’in.