An zabi dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen a matsayin gwarzon dan wasan Afrika a bangaren kasa da kasa ta masu shirya kyaututtukan kwallon kafar Ghana.
An sanar da nadin Osimhen ne a shafin hukumar bayar da kyaututtuka ta kwallon kafa ta Ghana a Twitter.
Dan wasan Liverpool da Masar, Mohammed Salah shi ma an zabi shi ne tare da dan wasan Manchester City da Algeria, Riyad Mahrez.
Osimhen ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya buga wanda ya taimakawa Napoli lashe gasar Scudetto a karon farko cikin shekaru 33.
Dan wasan mai shekaru 24 ya kuma zura kwallaye biyar a gasar zakarun Turai.
Dan wasan na Najeriya ya samu kyautar dan wasan da ya fi zura kwallo a raga, sannan kuma an ba shi kyautar dan wasan gaba a gasar.
A nasa bangaren Salah ya ci kwallaye 30 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 16 a wasanni 51 da ya bugawa Liverpool.
Shi ma Mahrez ya zura kwallaye 15 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 13 a wasanni 47 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga wa Manchester City.