Majalisar dokokin Ghana ta soke hukuncin kisa, bayan da amince da yin gyara ga dokar hukumar manyan laifuka ta 2022. Ya biyo bayan tsawon lokaci na hanƙoro daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na ganin an yi watsi da dokar.
Lauya mai hanƙoron kare hakkin dan’adam kuma dan majalisa Francis-Xavier Kojo Sosu ne ya miƙa wa majalisar kudirin dokar domin sauya ta tare da goyon bayan wata kungiya da ke Birtaniya mai rajin ganin an yi watsi da hukuncin kisa (Death Penalty Project).
Ya ce “A kan hukuncin kisa, fursunoni suna farkawa da tunanin cewa wannan ita ce ranarsu ta ƙarshe a duniya. Sun kasance kamar matattu masu rai, sun daina yi kamar mutane saboda haka soke hukuncin kisa zai nuna cewa a matsayinmu na al’umma mun kuɗuri aniyar cewa ba za mu kasance masu cin mutunci ko haifar da rashin zaman lafiya ba.”
A halin yanzu akwai maza 170 da mata 6 da aka yanke wa hukuncin kisa, waɗanda a yanzu za a maye gurbin hukuncin da daurin rai da rai.
Ko da yake kotuna a Ghana sun zartar da hukuncin kisan ne kan waɗanda aka samu da laifin kisan kai da yunkurin aikata kisa da kisan kare dangi da kuma fasa-ƙwaurin zinare; ba a cika aiwatar da hukuncin ba. Ghana ta zartar da hukuncin kisa na ƙarshe ne a shekarar 1993.
Kungiyoyin kare hakki sun yi ta fafutukar ganin an soke dokar. Ɓangarori da dama na yaba wa ƙasar kan matakin soke hukuncin na kisa. In ji BBC.
Babbar jami’ar diflomasiyyar Birtaniya a Ghana Harriet Thompson, ta ce “Ghana ta shiga cikin dangin ƙasashen Commonwealth da suka dauki wannan mataki mai cike da tarihi.”
Birtaniya na adawa da hukuncin kisa a kowane hali kuma ta ce suna tare da Ghana a wannan batu.”