Hukumomin lafiya a kasar Ghana, sun sallami mutum 31 daga cikin 98 da aka killace su saboda cutar Marburg.
Wannan na zuwa ne bayan da mutanen suka shafe tsawon mako uku ba tare da nuna alamun cutar ba.
Hukumar lafiyar kasar ta ce alamomin cutar na bayyana ne daga kwana biyu zuwa mako uku.
Haka kuma kungiyar likitocin kasar ta yi kira ga al’umomin kasar da su bi matakan kariya domin takaita yaduwar cutar. In ji BBC.
Shugaban kungiyar Titus Beyuo ya ce, “Ya kamata mu kara mayar da hankali wajen kare kai daga wannan cuta saboda tana da saurin yaduwa”.