Reshen hukumar shige da fice na kan iyakar Seme a Najeriya ya ce Ghana ta tasa ƙeyar mutum 16 ‘yar Najeriyar zuwa gida saboda zargin su da aikata laifukan zamba ta intanet.
Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito kwantirolan rundunar, Chukwu Emeka, yana faɗa a ranar Juma’a yayin taron manema labarai cewa matasa ne da suka fita daga Najeriyar don neman sana’o’in da za su riƙe kan su.
“Hukumomin Ghana na zargin su da aikata laifukan zamba, amma binciken farko-farko da muka gudanar ya nuna wasu daga cikinsu yaudararsu aka yi suka shiga harkokin sakamakon haɗamar da matasanmu ke da ita ta yin arziki cikin gaggawa,” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa: “An yaudari wasu daga cikinsu cewa za su yi arziki nan take idan suka bar Najeriya. Sai dai abin baƙin ciki shi ne ba su tarar da abin da aka yi musu alƙawari ba a Ghana.
Mista Emeka ya shawarci ‘yan Najeriya su dinga yin balaguro da takardun da suka dace ta yadda za su samu damar zama su yi sana’ar da suke so a ƙasashen da suka je ta hanyar bin doka da oda.