Hukumomin lafiya a kasar Ghana sun killace mutum 34, saboda barkewar cutar Marburg mai alaka da cutar Ebola wacce ke saurin yaduwa.
An killace mutanen ne bayan sun yi mu’amala da mutunen da ake zargi cutar ta kashe.
Hukumomin sun ce suna sanya ido game da barkewar cutar Marburg a kasar, wacce aka bayyana samunta a wurare biyu a yankin Ashanti da ke kudancin kasar.
A wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar, ta ce mutum biyu ne suka mutu bayan da gwaji ya tabbatar suna dauke da kwayar cutar.
Jami’an daga hukumar lafiya ta duniya tare da hadin gwiwwar likitocin kasar suna fadada bincike tare da yin aiki tukuru domin ganin cutar ba ta yadu ba.