Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila, Steven Gerrard ya tafi Istanbul don tattaunawa da Trabzonspor.
Gerrard bai da aiki tun bayan da Aston Villa ta kore shi a ranar 20 ga Oktoba.
Dan wasan mai shekaru 42 bai kai shekara daya a matsayin kocin kungiyar ta Premier ba, bayan da ya koma daga Rangers ya fara aiki a gasar firimiyar Ingila.
An danganta Gerrard da aikin Poland a farkon wannan shekarar, bayan da hukumar FA ta kasar ta yanke shawarar kin sabunta kwantiragin Czeslaw Michniewicz.
Amma daga baya Poland ta nada Fernando Santos.
A cewar kafar yada labaran Turkiyya Karar, Gerrard ya ziyarci Istanbul a farkon wannan mako domin cin abincin dare tare da Ertugrul Dogan, wanda ke neman zama shugaban Trabzonspor.
Kungiyar tana matsayi na shida a gasar Super Lig ta kasar Turkiyya, bayan da ta samu nasara a wasanni 11 cikin 23 da ta buga.
Rahotanni sun ce Dogan ya yi alkawarin daukar Gerrard a matsayin koci idan ya lashe zabe mai zuwa.