fidelitybank

Gawuna ne ya kamata ya maye gurbi na – Tsohon Minista

Date:

Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya kamata a bai wa muƙamin minista bayan sauke shi.

A wata hira da BBC ya ce tsohon ministan ya ce dalilin da aka bayar na sauke shi, shi ne wai yankin Kano ta arewa da ya fito, ‘yan siyasa masu muƙamai a tarayya sun yi yawa don haka ana son mayar da kujerarsa yankin Kano ta tsakiya.

”Kuma indai da gaske ake kano ta tsakiyar za a yi wa, ai ga ɗan takararmu nan na gwamnan – wanda shi ne jagoranmu a yankin Kano ta tsakiyar, me zai hana a ba shi”?

Ya ce muƙamin da ka bai wa Gawuna a yanzu, ba zai iya riƙe magoya bayansa da shi ba.

”Kuma duka sauran takwarorinsa da suka yi takara a wasu jihohin an ba su muƙamai, misali ga ɗan takarar jihar Plateau, da na Zamfara duk, an ba su minista”, in ji T Gwarzo.

Ya ƙara da cewa ya kamata a fara yi wa Gawuna tayin muƙamin, sai dai in shi ne ya ce ba ya so, to sai a bai wa wani.

”To amma shi ma wannan da aka bai wa ni bani da wani haufi da shi, tare muke komai a siyasa kuma ina yi masa fatan alkairi”.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp