Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, a ranar Asabar, ya ce, jam’iyyarsa na tattaunawa da jam’iyyar Labour da kuma dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, kan yiwuwar kafa kawancen hadin gwiwa a babban zaben badi.
“Gaskiya muna tattaunawa da Peter Obi kuma wani kwamiti yana aiki don duba yadda za a yi hadaka a tsakaninmu.
Abokai da ’yan uwa suna ta tafe suna tattaunawa kan shirin hadewar,”. Kwankwaso ya kara da cewa.
Hadakar dai tana da muhimmanci domin kamar yadda kuke gani jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, ba su zabi ‘yan takarar su daga yankin Kudu maso Gabas ba, inji Kwankwaso.
Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso tana da dimbin magoya baya a Arewacin kasar nan, musamman yankin Arewa maso Yamma yayin da Mista Obi ya fice daga PDP kwanan nan ya koma jam’iyyar Labour Party.
Sai dai kuma, a bisa ka’ida ba abu ne mai yuwuwa a yi hadakar tsakanin bangarorin biyu, kafin babban zaben shekara mai zuwa.