Shahararren ɗan wasa Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa gasar kwallon kafa ta Saudiyya ta zarta Ligue ta Faransa a halin yanzu.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a bikin karrama gwarazan ƴan wasa na Globe Soccer wanda aka yi a Dubai.
Ronaldo wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na Gabas ta Tsakiya a bikin, ya ce yana da tabbacin gasar ta Saudiyya ta bunƙasa bayan shekara ɗaya da ya shafe a can, kuma ƙungiyoyi na fafatawa sosai.
“A gaskiya, ina ganin gasar Saudiyya ba ta fi ta Faransa muni ba. Muna da kyau fiye da gasar Faransa a yanzu,” in ji Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar.
Ronaldo shi ne babban ɗan wasa na farko da ya fara komawa Saudiyya lokacin da ya kulla yarjejeniya da Al-Nassr a watan Janairun bara.
Ya ce yana da yakinin cewa nan gaba kaɗan gasar Saudiyya za ta zama ta uku a duniya, inda ya ce mutanen Saudiyya za su yi alfahari da hakan.
“Na fi kowa zura kwallaye a shekarar 2023, ina da shekara kusan 39… abin alfahari ne doke matasan ƴan kwallo irinsu Haaland,” in ji Ronaldo.
Gasar ta Saudiyya ta haɗa zaratan ƴan wasan kwallon kafa na duniya irin su Karim Benzema na Faransa, da Neymar na Brazil da kuma ɗan wasan Senegal Sadio Mane waɗanda duka suka bar Turai domin komawa ƙasar.