An haramta sayar da barasa a filayen kwallon da Qatar za ta karbi bakwancin wasannin cin kofin duniya.
Za ake rinka shan barasar ne a wasu kebabun wurare da aka ware, domin takaita shan barasar a kasar da ke bin dokokin Musulunci.
A ranar Lahadi za a soma gasar inda Qatar za ta buga wasan farko da Ecuador.
Qatar dai na cigaba da daukar matakai da bijiro da tsare-tsaren faranta ran manyan bakinta gabanni soma wasanni.