Ofishin babban mai binciken kudi na tarayya (AuGF) ya bayyana cewa a yanzu NNPC Limited, ya gaza yin lissafin kusan ganga 107,239,436.00 na danyen mai da aka dago don amfanin cikin gida a shekarar 2019.
Har ila yau AuGF ta ce, bayanan da aka samu daga rahoton ayyukan dakunan ajiya guda biyu sun nuna cewa, kimanin lita 22,929.84 na PMS da darajarsu ta kai Naira biliyan 7.06 da aka zuba a gidajen ajiyar guda biyu (Ibadan-Ilorin da Aba-Enugu) tsakanin watan Yuni da Yuli 2019 ba su samu ba.
Wannan fallasa ta kasance wani bangare ne na tambayoyi shida na tantancewa daga babban mai binciken kudi na tarayya, kamar yadda yake kunshe a cikin gwamnatin tarayyar Najeriya ta tattara bayanan kudi na shekarar da ta kare a ranar 31 ga watan Disamba, 2019 da aka mika wa magatakardar majalisar ta kasa ta wata wasika mai dauke da kwanan wata 18 ga watan Agusta, 2021, kuma babban mai binciken kudi, Adolphus Agughu ya sanya wa hannu.
Rahoton ya gano bambance da ke tsakanin adadin da NNPC ta bayar na mikawa asusun tarayya da kuma abin da AuGF ta ruwaito.
Ya ce yayin da bayanan NNPC ya nuna cewa N1,272,606,864,000.00 da kamfanin ya aika, adadin da Akanta Janar na tarayya ya rubuta ya kai N608,710,292,773.44, wanda ya nuna sabanin N663,896,567,227.
AuGF ta ce kamata ya yi a nemi Manajan Daraktan Rukunin na NNPC da ya yi bayanin sabanin da ke tsakanin wadannan alkaluman tare da tura ma’auni na N663,896,567,227.58 ga asusun tarayya ko kuma a hukunta shi.A cewar rahoton Tribune.