Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar wa al’umma cewa, za ta kammala dukkan shari’a kan hukuncin da aka yanke wa Abdulmalik Tanko da Hashimu Isiyaku, wadanda suka kashe Hanifa Abubakar.
Da yake mayar da martani a taron manema labarai a ranar Alhamis, babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a a Kano, Musa Abdullahi Lawan ya kawar da damuwar jama’a kamar yadda ya tabbatar wa Gwamna Ganduje a shirye yake ya cika alkawarin da ya dauka.
Lawan ya tunatar da cewa, duk da cewa hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ce, ke da alhakin bayar da takardar shaidar, ya ce, za a ba da irin wannan tanadin ne kawai bayan cikar kwanaki 90 na daukaka kara.
Babban Lauyan ya bayyana cewa, duk da hukuncin da aka yanke, mutanen biyu da aka yankewa hukuncin suna da damar neman daukaka kara kan hukuncin da karamar kotu ta yanke.


