fidelitybank

Ganduje ya yi wa Fursunoni 12 afuwa bayan an yanke musu hukuncin kisa

Date:

Gwamna Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa wasu fursunoni 12 da aka yanke wa hukuncin kisa afuwa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da gidan ajiya da gyaran hali na jihar, SC Musbahu Lawan Nassarawa ya fitar, ta ce gwamnan ya yi wa ɗaurarrun afuwa ne duba da irin cunkoso da ake samu na waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa.

Ya ce, tun da farko an yi niyyar yi wa fursunonin afuwa tun a bara, amma hakan bai yi wu ba, saboda sai da aka ɗauki lokaci aka tantance su.

Ya kuma ce, a yanzu an samu sauki na raguwar mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a gidajen yari, bayan afuwa da gwamnan ya yi wa wasu daga cikinsu.

Gwamnan ya kuma yafewa wasu fursunoni mata guda huɗu waɗanda suka shafe tsawon shekaru a ɗaure, saboda ganin kyakywan hali da suka nuna a lokacin da suke ɗaure.

An yi kira gare su da su zamo mutane masu kirki bayan komawa cikin al’umma da kuma cewa su guji duk abin da zai sake sa su koma gidan gyaran hali.

Sanarwar ta ce, wasu fursunonin da aka yi wa afuwa sun shafe shekaru 25 suna jiran aiwatar da hukuncin kisa a kansu.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp