fidelitybank

Ganduje ya yi garambawul a gwamnatinsa

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, ya amince da nadin Malam Usman Muhammad a matsayin shugaban ma’aikata na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Abba Anwar ya fitar jiya.

Anwar ya ce, gwamnan ya kuma amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda hudu a ma’aikatan gwamnatin jihar.

Ya ce, Muhammad ya kasance babban sakatare a ma’aikatar yada labarai kafin nadin nasa.

Sabbin Sakatarorin Dindindin sun hada da Muhammad Shehu, wanda har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne Daraktan Bincike da Kididdiga na Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar (KARMA).

Sauran su ne,vMalam Magaji Lawan wanda shi ne Daraktan kudi da asusu na ma’aikatar kudi kafin nadin sa.

Saura biyun su ne, Bilyaminu Zubairu, da Malama Mairo Dambatta,” in ji Anwar.

Yace nade-naden ya fara aiki ne nan take.

nigeria.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp