Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Baffa Babba Ɗan’agundi a matsayin shugaban hukumar kare haƙƙin masu saye da sayarwa a jihar Kano.
Bai wa Alhaji Baffa mukamin ya zo ne bayan tabbatar da jajircewarsa wajen riƙe mukamin da ya yi a baya.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce bai wa Baffa muƙamin zai fara aiki ne nan take.
Alhaji Baffa Ɗan’agundi shugaban hukumar Karota a Kano, zai ci gaba da rike mukaman biyu tare da aiki tare.
Sai dai mukamin shugaban hukumar kare haƙƙin mai saye da sayarwar da aka bai wa Baffa na riƙo ne.