Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a kan dokar inganta rayuwar masu bukata ta musamman, wadda majalisar dokokin jihar ta zartar kwanan nan.
Gwamnan ya ce dokar za ta taimaka wajen sanya masu larurar nakasa a cikin tsare-tsaren gwamnati da suka shafi cigaban kasa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce wanzuwar wannan doka ta inganta rayuwar masu larurar nakasa za ta ba da damar fito da wannan bangare na al`umma da nau’o’in bukatunsu ta yadda za a shigar da su a cikin tsarin gwamnati, tare da share musu hawaye.
Dokar ta hana yi musu kallon kaskanci, sannan ta yi tsari na saukaka musu rayuwa wajen shige da fice a gine-gine da ma’aikatun gwamnati – ga kuma tanadin da ya ti na kaso na musamman na guraben aiki domin masu larurar nakasar.
Malam Yerima Sulaiman Ibrahim na cikin shugabannin masu bukata ta musamman din a Najeriya, kuma daya daga cikin jagororinsu a jihar Kano, wanda ya ce suna murmushi har kunne, sakamakon sanya hannu da gwamnan ya yi a kan wannan doka.
Sai dai ganin cewa gwamnan ya rattaba hannu a kan wannan dokar ne a wata gaba da wa’adin mulkinsa ke karewa.
Wannan ne ya sa Malam Yerima Sulaiman ya ce, mutanensa na so gwamnan ya yi wani abu kasa da zai sa hukumar kula da masu larurar nakasar ta dore har bayan zamaninsa:
A makon jiya ne majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wannan doka ta inganta rayuwar masu bukata ta musamman din.
Sai ga shi a wannan makon gwamna Ganduje bai tsaya wata-wata ba–ya rattaba mata hannu.
Wadanda aka yi dokar domin su sun hada da masu larurar rashin gani, rashin kafa ko hannu, da larurar ji, da ta fata ko zabiya da larurar rashin yatsa wato kuturta da masu cutar laka da kuma galahanga.