Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya mika sunayen sunayen kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Kakakin majalisar, Hon. Hamisu Chidari ya karanta wasikar gwamnan a zauren majalisa ranar Litinin.
Sunayen wadanda aka nada sune, Ibrahim Dan’azumi Gwarzo, Abdulhalim Liman Dan Maliki, Lamin Sani Zawiyya, Ya’u Abdullahi Yanshana, Garba Yusuf Abubakar, Yusuf Jibril Rurum, Adam Abdu Panda da Saleh Kausani.
Solacebase ta bayar da rahoton murabus din kwamishinonin guda takwas gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa a cikin wadanda ke da sha’awar tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.


