fidelitybank

Ganduje ya mika kunshin kasafin kudi Naira biliyan 245.3

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kudirin kasafin kudi na Naira biliyan 245.3 ga majalisar dokokin jihar na shekarar 2023.

Wanda aka yiwa lakabi da Budget for Consolidation and Prosperity II, kididdigar sun haura Naira biliyan 49, sama da kasafin kudin 2022, kuma za a bi su ne ta hanyar kason kudi, tallafi, lamuni da IGR.

A shekarar da ta gabata Ganduje ya gabatar da sama da Naira Biliyan dari da casa’in da shida (N196b) ga majalisar dokokin jihar Kano, na shekarar 2022.

Kudirin kasafin kudi na shekarar 2023 da aka gabatar yana da Naira biliyan 144.6 a matsayin babban kashe kudi wanda ke wakiltar kashi 59 cikin 100 na jimillar kasafin kudin, yayin da kudaden da ake kashewa akai-akai a cikin kudirin da aka gabatar ya kai sama da Naira biliyan 100, wanda ke wakiltar kashi 41 cikin 100 na girman kasafin.

Kunshin kasafin dai shi ne na karshe na irin wannan gabatarwar da Ganduje ya yi a gaban majalisar dokokin jihar, domin a watan Mayun shekara mai zuwa ne ake sa ran zai mika mulki.

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp