Gabanin zaben gwamnan jihar Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Yomi Awoniyi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki a hukumance.
A makon da ya gabata Awoniyi ya mika takardar murabus din sa ga jam’iyyar adawa ta PDP.
Awoniyi ya samu tarba a hukumance cikin jam’iyyar APC a hedikwatar jam’iyyar ta kasa ranar Talata a Abuja.
Da yake jawabi jim kadan bayan bayyana sabuwar tafiyarsa ta siyasa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi ya amince da sarkakiya da kalubalen siyasar jihar ta Kogi.
Ya yabawa Gwamna Bello bisa yadda ya hada jihar Kogi a kan duk wata matsala.
Ya ce: “Na yi Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015. Na san jihar sosai, kuma zan iya gaya muku cewa Gwamna mai ci ya yi nagartaccen aiki na musamman ta fuskar shugabanci da shugabanci na gari. Tawali’unsa ba ya misaltuwa, kuma iyawar sa na hada kan jama’a na da ban mamaki.
Awoniyi ya rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Kogi daga shekarar 2011 zuwa 2015 a lokacin gwamnatin Captain Idris Wada.
Gwamna Yahaya Bello, yayin da ya ke karbar Awoniyi, wanda ya bayyana a matsayin “babban kifi”, ya ce shawararsa ta komawa APC na da matukar muhimmanci.


