Tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar gudanarwar ma’aikatar kula da filayen jirgin sama ta Najeriya, FAAN.
Gbenga Saka, mataimaki na musamman ga ministan ma’aikatar a fannin yaɗa labarai, Gbenga Saka ne ya tabbatar da hakan a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.
An yi bikin raka shi Ofis a Abuja, makonni bayan Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC.