Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kai ziyarar duba aikin ginin katafariyar gadar nan mai hawa uku wacce babu irinta a fadin Najeriya, mai suna Muhammadu Buhari Interchange, wacce ake ginawa a shataletalen Hotoro, NNPC Roundabout.
Ana dab da kammala aikin gadar mai hawa uku wacce akewa laƙabi da “karshen zance”.
Da zarar an kammala za ta saukake yanayin chunkoson da ake fama dashi a wannan shataletalen, inda zai kara bunkasa harkokin kasuwanci kasancewarta babbar hanyar da mutane daga makwabtan jihohi ke shigowa Jihar Kano domin harkokin kasuwancin su.