Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kaddamar sashin kula da kananan yara mai Gado Ashirin da Biyar (25 Beds Capacity ITFC) a Unguwa Uku Karamar Hukumar Tarauni.
Gwamnan ya kuma kaddamar da sashin haihuwa wato (Abdullahi Muazu Maternity Complex)a Asibitin Waziri Gidado dake Bachirawa, Karamar Hukumar Dala.
Kwamishinan lafiya Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya jagoranci bude ayyukan tare da Shugabbannin Kananan Hukumomin Tarauni Hon. Abubakar Zakari dana Karamar Hukumar Dala Hon. Ibrahim Dan Isile da Shugaba Karamar hukumar Ungogo Hon. Abdullahi Garba Ramat.