Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga Landan a jiya Laraba.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya tafi ƙasar Birtaniya domin neman magani jim kaɗan bayan murabus ɗinsa daga shuagabancin jam’iyya mai mulki a ƙasar.
Da ya ke tabbatar da wannan batu ga jaridar The PUNCH, tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba, ya ce Ganduje ya sauka a Nijeriya ne a safiyar jiya Laraba bayan shafe kusan wata guda a waje.
Gwamna Abba ya rantsar da sabon shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa ta Kano
“Eh, ya dawo Najeriya yau. Ya dawo cikin koshin lafiya, kuma ya ƙarasa gidansa,” in ji Garba.
Ya ƙara da cewa Ganduje ya bar Najeriya zuwa Landan ne kwana biyar bayan ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar domin neman lafiya.