fidelitybank

Ganduje ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta binciki gwamna Abba

Date:

Wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai a jihar Kano, tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC da kuma gwamnan Kano na yanzu na jam’iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje a cikin wata sanarwa, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da furta kalaman tunzura jama’a a gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar ‘yan kwanakin da suka gabata a duk fadin kasar nan.

Sai dai ɓangaren gwamnan na Kano ya yi watsi zargin wanda ya kira “soki burutsu”.

Tun hawa kan mulki, gwamnatin Kano ta NNPP ke takun saƙa da tsohon gwamnan jihar na jam’iyyar APC da ta gada.

Tsohon gwamnan na Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani ne ga zargin da gwamnatin Kano ta yi cewa shi ya yi hayar ƴan daba domin haifar da rikici a jihar a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar.

A cikin sanarwar da Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fitar ranar Alhamis, ya zargi gwamnan Abba Kabir Yusuf da yin kalaman da suka ingiza jama’a ga yin tarzoma da nufin baƙanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Yakamata gwamnatin tarayya ta binciki gwamnatin jihar Kano domin kowa ya san cewa kafin zanga-zangar, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kalamai na tunzura jama’a, saɓani matakan da sauran gwamnonin jihohi suka ɗauka,” in ji Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai tun da farko gwamnatin jihar Kano ta zargi tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin wasu matasa da suka fasa kotu tare da sace takardun shari’oi.

“Kowa ya ga yadda mutanen Ganduje suka shigo Kano suka raba wa matasa makamai da kuɗaɗe da kayan shaye-shaye waɗanda suka far wa ɓangarori da dama na al’umma, lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi,” in ji Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano.

Sanarwar da gwamnatin Kano ta fitar ranar Laraba ta ce cikin takardun da aka kwashe har da na shari’ar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatin jihar ke tuhumarsa da matarsa Hafsat da ɗansa Umar, da wasu mutum biyu bisa zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.

Kuma a cikin martaninsa a ranar Alhamis, tsohon gwamnan ya yi watsi da zargin wanda ya danganta da yunƙuri na “ci gaba da yi masa bita da ƙullin siyasa.”

“Wannan kawai wani yunƙuri ne gwamnatin Yusuf na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga rikicin da ya faru a jihar,”

“Maganar cewa za a iya kwashe irin waɗannan muhimman takardu yayin zanga-zanga, ya ƙara nuna fito da gazawar wajen tafiyar da harkokin tsaro da na shari’a,” in ji Ganduje.

Wannan sabuwar sa’insa dai wata alama ce da ke nuna yadda takun saka ke dada munana tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Kano da wanda ya gaje shi.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp