Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kudi Naira miliyan 3.8 ga iyalan mutane 19 da suka yi hatsarin mota a tsakanin hanyar Zariya zuwa Kano, a kauyen Tusguri da ke unguwar Sanda, a karamar hukumar Bunkure.
Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya bayar da kudin, ya c,e Naira 200,000 na kowane iyalan wadanda suka ransa, da suka kone kurmus, a hanyarsu ta dawowa daga Ilorin.
Ya ce, “Mun samu rasuwa cikin kaduwa kuma muna addu’ar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gafarta musu dukkan kurakuren su, ya saka musu da Aljannah.”
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, Kwamared Abba Anwar, kwafin da aka rabawa manema labarai a Kano ranar Lahadi.
Ganduje ya kuma umurci shugaban karamar hukumar da ya rubutawa gwamnatin jihar tare da neman a gina makarantar firamare a yankin wanda ya yi alkawarin gaggauta daukar mataki.
A cewarsa “domin taimakawa al’ummar yankin wajen noman noman rani, “…Ina tabbatar muku da cewa, gwamnatin tarayya ta sa baki wajen noman rani, wannan garin zai kasance cikin shirin.