fidelitybank

Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami

Date:

 

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Aliko Dangote, Aminu Dantata da Abdussamad Isyaku Rabiu a matsayin mambobi na kwamitin gudanarwa na Hukumar Zakka da Hubusi ta Kano.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, inda ya ce naɗin ya samu ne bayan taron Majilisar Zartsawa na Mako-mako.

Ya ce Dr Ibrahim Muazzam Maibushira, shi ne a ka naɗa a matsayin Shugaban kwamitin.

Sauran, a cewar Kwamishinan, sun haɗa da Dr AbdulMutallab Ahmed a matsayin Kwamishina I sai kuma Dr Lawi Sheikh Atiq a matsayin Kwamishina na ll a hukumar.

Sauran sun haɗa da wakilan Masarautar Kano, wakilan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Wakilan Ma’aikatar Harkokin Addinai, sai kuma wakilan kasuwannin kurmi, Rimi, Kwari da Singa.

Hakazalika Garba ya sanar da cewa Majalisar Zartaswar ta sahale da kafa kwamitin da zai tantance Cibiyar Addinin Musulunci ta Duniya.

Ya ƙara da cewa Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen ne zai shugabanci kwamitin, inda Dakta Muhammad Tahar Adam, Kwamishinan Harkokin Addinai zai zama Shugaban na 2, sai Auwalu Yakasai a matsayin sakatare.

 

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp