fidelitybank

Ganduje ya baiwa Ahmad Lawan goyon baya

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya tabbatar wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan “cikakkiyar hadin kai” kan burinsa na tsayawa takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa na 2023.

Gwamna Ganduje ya bayyana jihar Kano a matsayin jaha mai zage-zage a zabukan fitar da gwani na jam’iyya har ma da zaben shugaban kasa ya kuma bayyana cewa jihar Kano za ta yi kaca-kaca idan ta shirya. In ji Politics Nigeria.

Ya yi wannan jawabi ne a daren Asabar a lokacin da Lawan ya kai ziyarar gani da ido a Kano gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa a karshen wannan wata.

Gwamna Ganduje da kansa ya tarbi Lawan da tawagar yakin neman zabensa a filin jirgin sama na Aminu Kano a daidai lokacin da dimbin magoya bayan jam’iyyar suka yi cincirindo a filin jirgin sama da tituna domin tarbarsu a tsohon birnin.

A jawabinsa na maraba, Gwamna Ganduje ya ce, al’ummar Kano sun san kyawawan halayen Lawan da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da dorewar siyasa da mulki a kasar nan.

Gwamnan ya ce, tun daga magabata na Lawan, idan ya ci zaben Shugabancin Najeriya, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a siyasa da mulki.

Ganduje ya shaida wa Lawan cewa: “Mai girma gwamna, ina so in sanar da kai cewa muna da cikakkiyar masaniya kan iyawarka. Muna sane da yadda kuke tafiyar da Majalisar Dokoki ta Kasa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, wadda ku ne shugabanta.

daily post newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp