A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Kano ta karbi bukatar a tantance karin kwamishina mai suna Dakta Ali Burum-Burum daga gwamna Abdullahi Ganduje.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Uba Abdullahi ya fitar a Kano.
NAN ta tuna cewa Ganduje, a ranar 15 ga watan Agusta, ya mika sunayen mutane takwas ga majalisar domin tantancewa tare da tabbatar da cike gibin da wasu ‘yan majalisar zartarwa na jihar suka yi na murabus dinsu na tsayawa takara a zaben 2023.
A cewar sanarwar, an aike da sunan karin wanda aka nada ne a wata wasika mai dauke da sa hannun Ganduje, wacce aka aike wa shugaban majalisar Hamisu Ibrahim-Chidari.
“Majalisa ta karbi wasikar a hukumance kuma a halin yanzu tana kan aiwatar da doka.
” Dr. Burum-Burum, tare da sauran kwamishinoni takwas da aka nada, za a tantance su ranar 22 ga watan Agusta. sanarwar ta ce.


