Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban Najeriya sanata Kashim Shettima na yunƙurin sasanta tsakanin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Sanata Rochas Okorocha gabanin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe.
Cikin wani saƙon ‘X’ da a baya aka fi sani da Tuwita, da APC ta wallafa ta ce ‘gabanin zaɓen gwamna da ke tafe a jihar Imo, APC gida ne na haɗin kai don ƙarfafa juna”.
Jam’iyyar ta kuma wallafa hotunan mutanen biyu na gaisawa da juna, ga kuma shugaban jam’iyyar da mataimakin shugaban ƙasar.
Mutanen biyu waɗanda su ne jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar sun samu saɓani tsakaninsu, inda suka ƙwashe lokaci suna takun-saƙa.
A shekarar 2021 ne Uzodinma ya samu umarnin kotu wajen ƙwace wani kadarar Okorocha da ke jihar.
A lokacin Okorocha ya yi yuƙurin ɗaukaka ƙara, amma jami’an tsaro suka kama shi, kodayake an sake shi a ranar.
Saɓani tsakanin mutanen biyu ta faro ne tun a zaɓen 2019 a lokacin da Okorocha ya zaɓi bai wa surukinsa takarar gwamnan jihar, maimakon Uzodinma.
Lamarin da ya haifar da ‘yan takarar gwamna biyu a ƙarƙashin APC, sai dai daga baya uwar jam’iyyar ta ƙasa – ƙarƙashin Adam Oshimole – ta ce Uzodinma ne halastacen dan takara.
Tun bayan da ya zama shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Ganduje ya alƙawarta tabbatar da haɗin kan jam’iyyar, domin samun nasara a zaɓuka masu zuwa musamman na jihohin Imo da Kogi da kuma Bayelsa.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Imo.