fidelitybank

Ganduje da Kwankwaso su haɗe kan su don a ciyar da Kano gaba – Murtala Sule Garo

Date:

Domin a warware takaddamar siyasar Kano, kuma a samu hadin kai, dole ne mai girma tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje da magabatansa, Rabiu Kwankwaso da Ibrahim Shekarau, su kawar da sabanin da ke tsakaninsu, su hada kai domin ci gaban jihar.

Wannan shine matsayin tsohon kwamishinan al’amuran kananan hukumomi na jihar Kano kuma dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023, Murtala Sule Garo.

Ya bayyana damuwarsa kan rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin tsaffin gwamnonin jihar yayin da yake jawabi a wajen taron tsaffin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano na 8 da 9.

Garo ya yi kira ga Ganduje da Kwankwaso da su ajiye sabanin da ke tsakaninsu su hada kai domin ci gaban jihar Kano.

“Roƙona shi ne ga tsoffin gwamnoninmu. Abin takaici ne ganin yadda a Jiha irin ta Zamfara da ke bayan Kano ta fuskoki da dama, tsofaffin Gwamnonin nasu suna taruwa suna taro duk da bambancin siyasa da akidunsu. Suna ganawa da tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jiharsu.

“Amma a nan Kano, abin mamaki da ban takaici ne yadda shugabanninmu da dattawanmu, tsofaffin gwamnoni, ba za su iya haduwa don tattaunawa kan al’amuran da za su kawo ci gaban Kano ba.

“Saboda haka, muna rokonsu, kuma muna musu addu’a da su sasanta su kuma ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu idan da gaske suna son ci gaban jihar Kano,” in ji Garo.

Rikicin Ganduje da abokin siyasa kuma amininsa Kwankwaso ya faru ne nan da nan bayan zaben gwamna na 2015, wanda ya sa Ganduje ya samu nasara kuma ya zama magajin Kwankwaso.

punch newspaper headlines today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp