fidelitybank

Ganawar gwamnatin Najeriya da ta Nijar ko akwai alfanu?

Date:

Ministocin harkokin wajen Najeriya da Nijar sun gudanar da wata tattaunawa ta musamman kan al’amura da dama da suka shafi harkokin tsaro da tattalin arziki a kan iyakokin ƙasashen biyu.

Hakan dai na zuwa ne bayan da Najeriya ta sake sabunta kiraye-kirayen neman a saki hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, wanda ke tsare a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai.

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya tattauna da ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare, a ziyara ta biyu da wani babban jami’in Najeriya ya kai tun bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar a 2023, bayan Janar Christopher Musa, babban hafsan tsaron Najeriya ya ziyarci Nijar a watan Agustan bara,

”Tattaunawar ta gudana ne cikin yanayi mai cike da mutuntawa ta kuma bayar da damar yin nazari mai zurfi kan ƙalubalen da ƙasashen biyu ke fuskanta,” in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da ministocin biyu suka fitar.

A ɓangaren tattalin arziki, ministocin sun tattauna kan aikin layin dogo da zai haɗa garuruwan Kano da Katsina na Najeriya zuwa Maradi a Nijar, wanda za a buɗe a shekarar 2026.

Har ila yau, sun tattauna batun gina babbar hanyar Trans-Sahara, da shirin bututun iskar gas da za a yi a yankin Sahara, da kuma batutuwan da suka shafi haraji.

Nijar da Burkina Faso da Mali sun fice daga ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka a farkon wannan shekara, inda suka zargi ƙungiyar ECOWAS da gazawa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Dukkanin ƙasashen uku dai na ƙarƙashin jagorancin sojoji ne, kuma suna fuskantar munanan hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp