Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gaji bashin Naira biliyan 307 daga gwamnatin da ta shude a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karbar rahoton kwamitocin kan tsarin mika mulki da dabarun ci gaban jihar Filato a ranar Litinin a Jos.
Farfesa Ganyir Lombin ya jagoranci kwamitocin biyu.
Gwamnan ya bayyana aniyar sa na ganin jihar ta kai ga kololuwa duk da dimbin basussukan da ta ke.
Mutfwang musamman ya bayyana shirinsa na tunkarar kalubalen tsaro a jihar.
“A duk lokacin yakin neman zabe, mun kasance a karkashin kuskuren imani cewa bashin da ake bin mu ya kai kusan Naira biliyan 200; jin cewa Naira biliyan 307 abu ne mai ban tsoro da damuwa,” inji shi.
Gwamnan ya yi alkawarin yin nazari sosai kan takardar da aka gabatar masa, inda ya kara da cewa za a kuma gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace bayan haka.
Tun da farko, Lombin ya bayyana cewa, wasu kalubale na aiki sun hana kwamitocin biyu, wadanda suka nada na gwamnatin da ta gabata a matsayin mambobi, gabatar da rahotonsu tare.
Ya ce takardar mika mulki da aka mika wa gwamnan a ranar 29 ga watan Mayu ya sha banban da tsarin da kwamitin hadin gwiwa ya tsara.