fidelitybank

Gabon ta haramta wa jami’an gwamnati zuwa hutu kasashen waje

Date:

Shugaban Riƙon Ƙwarya na Gabon, Brice Oligui Nguema ya dakatar da jami’an gwamnatinsa na riqon ƙwarya tafiya hutu a ƙasashen waje, a wani yunƙuri da ya dace da tsarin shugabacinsa.

An bayar da sanarwar ce a wata wasiƙa da aka karanta a talabijin ɗin ƙasar, inda jagororin juyin mulkin suka sanar da cewa hutun mako ɗaya ne kawai jami’in gwamnati yake da shi a shekara.

“Dole a cikin kasar nan kowa zai yi hutunsa, sannan duk wanda zai yi hutu, asalin garinsa zai koma domin su riƙa shiga cikin harkokin mutanensu na yau da kullum,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Wannan na zuwa ne bayan Janar Nguema ya zagaya cikin ƙasar, inda ya tattauna da mutanen ƙasar, sannan ya saurari matsalolinsu.

“Wannan matakin zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar komawa gida, sannan zai ƙara kawo kusanci da mutane,” inji kakakin gwamnatin sojin, sannan ya ƙara da cewa za a iya samun akasin hakan ne kawai domin rashin lafiya ko kuma wani lamarin da zai iya zuwa ba zato ba tsammani.

Tun bayan da Janar Oligui ya yi juyin mulki daga tsohon Shugaban Ƙasar Ali Bongo a bara, ya dage wajen nuna wa mutanen ƙasar cewa gwamnatinsa ta mutane ce. Wannan matakin ne hana jami’an gwamnati tafiya hutu a ƙasashen waje na zuwa makonni ƙaɗan bayan shekara ɗaya da juyin mulkin da aka hamɓarar da Ali Bongo.

Haka kuma wadannan matakan suna zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Janar Nguema yana kamun ƙafa ne domin tsayawa takarar Shugaban Ƙasa, wanda ake sa ran za a yi a Agustan baɗi.

Sai dai har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ba.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp