Rahoton na ƙungiyar kare ƴan jarida ta duniya ya bayyana cewa, Gabas ta tsakiya ne yankin da aka fi cin zarafin ƴan jarida a faɗin duniya.
Rahoton ya ce “yanayin ya munana” a kusan rabin ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya.
Ƙasashen da lamarin ya fi ƙazancewa su ne: Yemen, Saudiyya, Iran, Yankin Falasɗinawa, Iraƙi, Bahrain, Syria da Masar.
Yankin Falasɗinawa shi ne wuri mafi haɗari ga ƴan jarida a faɗin duniya, kuma tana cikin ƙasashe na can ƙasa a ɓangaren kare ƴan jarida a duniya.
Ƙasashen da ƴan jarida suka fi samun ƴanci da sauƙin gudanar da ayyukansu kamar yadda rahoton ya nuna kuwa sun fi yawa ne a nahiyar Turai.
Ƙasa ta farko ita ce Luxembourg, sai Liechtensein a matsayi na biyu, yayin da Samoa take a matsayi na uku.