fidelitybank

Gabanin zabe PDP za ta karbi masu sauya sheka kwanan nan – Tambuwal

Date:

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar da tabbacin cewa, jam’iyyar PDP, za ta tarbi masu sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa gabannin zaben 2023.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, yayin ziyararsa ta uku kan neman shawara game da kudirinsa na neman tikitin shugaban kasa na PDP, a birnin Kebbi, jihar Kebbi.

Tambuwal wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da tsohon mataimakin gwamnan Sokoto Mukhtar Shagari da tsohon ministan lantarki, Injiniya Bello Suleiman, ya yaba da hadin kan da jiga-jigan PDP a Kebbi da mabiyansu suka nuna a zaben karamar hukuma da aka yi kwanan nan.

Tambuwal ya kuma koka kan yadda Najeriya ke shirin rugujewa, sakamakon rashin tsaro da tsarin kiwon lafiya mara inganci, talauci, tabarbarewar ilimi, cin hanci da rashawa da sauran yanayi da gwamnatin APC ta jefa kasar a ciki.

Bafarawa wanda ya bayyana ziyarar a matsayin na gida, ya nuna farin ciki da karamcin da PDP reshen jihar Kebbi ta nuna a yayin zaben kananan hukumomi a jihar.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp