Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa’id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa.
Cikin rahoton daEFCC ta fitar, kotun ta kama G Fresh da laifin “liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000” a shagon Rahama Saidu a watan Nuwamban 2024.
Kazalika, kotun ta kama Breaker da laifin “wulaƙanta takardun naira na N200 da suka kai N30,000” yayin wani biki a garin Hadeja da ke jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.
Mai Shari’a S.M Shuaibu ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya CBN ta 2007, kuma ya yanke wa kowannensu ɗaurin wata biyar a gidan yari ko kuma tarar naira 200,000.