Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da hukumar EFCC ta shigar gabanta, tana tuhumar tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha da zargin aikata laifukan da suka shafi almundahanar kuɗi.
Hukumar ta EFCCn dai na tuhumar tsohon gwamnan da aikata zambar kuɗi da amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba.
To sai dai kotun ta bayyana tuhumar da cewa tozarta tsarin shari’a ne.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya ce hukumar EFCC ta shigar da makamanciyar tuhuma a kan tsohon gwamnan a babbar kotun taraya, wadda a cikin watan Disamban da ya gabata ta yanke hukuncin da ya wanke tsohon gwamnan.


