An samu labarin tserewan fursunoni daga wani gidan yari da ke garin Goma a yankin gabashin Jumhuriyar Dimokradiyar Kongo, yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin ƴan tawayen M23 da dakarun sojin ƙasar.
Bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna mutanen da ake kyautata zaton fursunoni ne a titunan birnin, sa’o’i kaɗan bayan da mayaƙan ƙungiyar M23 masu ɗauke da makamai da sojojin Rwanda suka shiga babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa an yi tashe-tashen hankula a gidan yari da safiyar ranar Litinin wanda hakan ya yi sanadiyar tserewar fursunonin.
Rahotanni dai na bayyana cewa ƴan tawayen na daf da karɓe iko da Goma da ake cewa sun ƙwace filin saukar jirgin sama.
Gwamnatin Kongo dai ta dage cewa tana samun galaba yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a wasu sassan birnin.
Ana zargin ƙasar Rwanda da marawa ƙungiyar Tutsi ta M23 baya a yayin da take ci gaba kai hare-hare cikin ƴan watannin nan a faɗin yankin mai arzikin ma’adinai.
Rwanda ta sha musanta wannan zargi.