Wani fursuna ɗan ƙasar Falasɗinu ya rasu a gidan yarin Isra’ila sakamakon yajin cin abinci na kwana 86.
Khader Adnan babban ƙusa ne a ƙungiyar masu iƙirarin jihadi, wanda Isra’ila ta zarga da laifukan ta’addanci.
Hukumomin gidan yarin Isra’ila sun ce fursunan ya ƙi amincewa a yi masa magani, kafin a same shi cikin mawuyacin hali a ɗakin da yake ɗaure a gidan yarin ranar Talata.
Firaministan Falasɗinu ya zargi Isra’ila da kisan Adnan ”da gangan” yayin da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta yi barazanar ɗaukar fansa a kan isra’ila.
Adnan mai shekara 44 – wanda ke zaune a arewacin yamma da gaɓar kogin Jodan – ya kwashe fiye da shekara 20 ana ɗaure shi a gidajen yarin Isra’ila.
Sau huɗu yana shiga yajin cin abinci a baya, lamarin da ya sa sunansa ya yi fice a Falasɗinu.
Yajin cin abinci ga fursunonin Falasɗinu da ke ɗaure a gidajen yarin Isra’ila abu ne da aka saba gani, to sai dai a ‘yan shekarun baya-bayan nan an samu raguwar mace-macensu, sakamakon taimakon magani da aka ba su.