Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike, ya zargi Gwamna Sim Fubara na Jihar Ribas da cin dunduniyar jam’iyyar PDP tare da yi mata zafin ƙasa.
Wike ya ce Fubara ya goyi bayan jam’iyyar Action Peoples Party, APP, wajen lashe kujerar shugaban kasa a zaben kananan hukumomin da aka kammala a jihar.
Ministan ya yi magana a gidan Talabijin na Channels TV’s Politics A Yau Talata yayin da ya dage cewa bai taba shiga cikin ayyukan kin jinin jam’iyya ba.
Kafin zaben dai an yi ta takun saka tsakanin Wike da Fubara kan yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a jihar.
Sai dai Wike ya ce: “A yau mutane sun ce Wike ya ladabtar da shi saboda ya yi adawa da jam’iyya, amma na ce ban yi adawa da jam’iyya ba.
“Yau me ya faru? Gwamnan ya dauki nauyin APP kuma Bala Mohammed shine ya halarci bikin rantsar da shugabannin APP.
“Na ce ba zan goyi bayan rashin adalci ba kuma ba ni da uzuri da zan bawa kowa saboda PDP ta amince da abin da zan yi amma ya ki.”


