Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin zaman majalisar da ya kunshi ‘yan majalisar biyar masu biyayya gare shi.
Wannan lamarin na zuwa ne ‘yan sa’o’i kadan bayan da gwamnatin jihar ta fara rusa ginin Majalisar.
Idan za a iya tunawa, ‘yan majalisar 27 da ke biyayya ga Ministan babban birnin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
‘Yan majalisar 27 ba su halarci taron ba a lokacin da gwamnan ya gabatar da kasafin a ranar Laraba.