Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya jaddada cewa dole ne gwamnan jihar Ribas Sim Fubara da tsohon gwamnan kuma ministan birnin tarayya Nyesom Wike su sasanta kansu, domin su ciyar da jihar gaba.
Tsohon Shugaban kasa Jonathan, ya bayyana damuwarsa kan kalubalen da ke tattare da rikicin da ya dabaibaye jihar Rivers.
Jonathan ya bayyana haka ne a yayin da ya kasance a matsayin babban bako na musamman a wani taron da gwamnatin jihar Ribas ta shirya domin kaddamar da aikin titin Trans-Kalabari a yau Litinin.
Goodluck Jonathab ya bayyana cewa, yayin da al’amura sukan taso a lokacin mika mulki daga wani Shugaba, zuwa wani shugaban wanda hakan ke zama abu mai radadi.
Da yake jawabi a jihar Ribas, Jonathan ya jaddada wajabcin yin hadin gwiwa tsakanin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da gwamna Sim Fubara, inda ya jaddada illar da tashin hankali ke haifarwa a yankin da ke da muhimmanci a matsayin tsakiyar yankin Neja Delta.