Tawagar Flying Eagles ta Najeriya, ta bar kasar nan ne a daren Asabar, domin yin atisayen makwanni biyu a kasar Argentina, domin tunkarar gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2023.
‘Yan wasa 20 da masu horar da ‘yan wasa sun yi tattaki zuwa Bueno Aires na kasar Argentina don yin atisayen sansani.
Ana sa ran dan wasan tsakiya na AC Milan, Victor Eletu zai hade tare da tawagar a Kudancin Amurka ranar Lahadi (yau).
Kungiyar Flying Eagles za ta nufi Mendoza bayan zamansu a babban birnin kasar.
Tawagar Ladan Bosso za ta fuskanci bude wasanni biyu a Mendoza.
Wasan karshe na rukuni na biyu da Brazil zai gudana ne a La Plata.
Argentina ce za ta karbi bakuncin gasar daga ranar 20 ga Mayu zuwa 11 ga watan Yuni.