Kocin Flying Eagles, Ladan Bosso ya mika gayyata ga masu tsaron gida biyu daga gasar Premier.
Wani rahoto da jaridar SCORENigeria ta fitar ya bayyana cewa, masu tsaron ragar sun hada da Ovie Ejeheri na Arsenal da Owen Goodman na Crystal Palace.
Kwanan nan Goodman ya kulla kwantiragin ƙwararru tare da Crystal Palace bayan ya zo ta makarantar kulab ɗin London.
Kwanan nan Ejeheri ya koma Arsenal bayan aro a Chelmsford City.
An zabi dan wasan mai shekaru 19 a matsayin gwarzon dan wasan watan Disamba na Chelmsford City.
Goodman da Ejeheri za su fafata da wasu masu tsaron gida uku, Nathaniel Nwosu, Saheed Jimoh da Chijoke Anigbaso, domin samun gurbi a kungiyar.
Ana sa ran Bosso zai fitar da jerin sunayensa na karshe a gasar a ranar 20 ga watan Janairu.