‘Yan wasan Flying Eagles sun sake yin kyakykyawan zato yayin da suka lallasa kungiyar kwallon kafa ta Deluxe da ci 6-0 a wasan sada zumunta da suka yi a Abuja da safiyar Juma’a.
Ba a samu nasarar zura kwallo a raga ba a farkon wasan duk da cewa bangarorin biyu sun samu damar zura kwallo a raga.
Kyaftin Ibrahim Yahaya ne ya fara zura kwallo a ragar Flying Eagles mintuna biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci.
Dan wasan gaba Haliru Seriki ya zura ta biyu a minti na 50 da fara wasan.
Dan wasan Remo Stars Adams Olamilekan ne ya kara ta uku mintuna uku kafin a tashi daga wasan.
Seriki ya zura ta hudu, inda Emmanuel Ochegbu ya kara kwallo biyu.
Yanzu haka dai kungiyar ta Flying Eagles za ta karkata ga wasan sada zumunta da za ta yi da Zambia.
Za a gudanar da wasannin sada zumunta ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranakun 3 da 6 ga watan Fabrairu.